Farin wata kyal-kyal / Moon Song

kodayaushe
dandalin wasa
tsit yake
 
tsit
kamar yadda
in kasuwa ta ci ta watse
 
a daidai lokacin da fatalwa
ke bayyana
kamar ka taba, ta yi magana
 
kai ka ce
muryar zabiya ce
a dandali.
 
tsit irin wannan
sai ko kogi
in ya ci kasuwa bayan makauniyar iska.
 
Sai ko in dare
sadaukin nan
ya ci dununmu da yaki
 
tamkar yadda ruwa ke lamusa
 
 

after
the playhouse
goes

quiet
in a similar way
a market does

a ghost
comes out
of its resonance

of the utmost
note
in the opera

only a
lake is quiet
as bare souk

& darkness
conquers
in a similar way

as water.
 
 
 
 
Translated from English into Hausa by Ibrahim Malumfashi